IQNA

An Gudanar Da Wani shiri Na Bayar Da Horo Kan Rubutun Musulunci A Pakistan

14:25 - February 20, 2011
Lambar Labari: 2083969
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da wani shiri na bayar da horo kan rubutun musulunci da kyautata shi a birnin Islamabad fadar mulkin kasar Pakistan, wanda ya yi daidai da lokacin gudanar da bukukuwan maulidin manzon Allah (SAW) da musulmi suke yi a ko’ina cikin fadin duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na The News an bayyna cewa, an gudanar da wani shiri na bayar da horo kan rubutun musulunci da kyautata shi a birnin Islamabad fadar mulkin kasar Pakistan, wanda ya yi daidai da lokacin gudanar da bukukuwan maulidin manzon Allah (SAW) da musulmi suke yi a ko’ina cikin fadin duniya domin raya wadannan ranaku masu albarka.
Wannan shiri ya samu halartar dalibai masu sha’awar koyon rubutun larabci da kuma ayoyin kur’ani da ake kawatawa a kan alluna da kuma takardu, da nufin kara karfafa su domin yada koyarwar addnin muslunci da kuma al’adunsa atsakanin al’ummar kasar, wadanda mabiya addinin musulunci ne.
Ma’aikatar kula da ayyukan muslunci musulunci tare da hadin gwiwa da ma’aikatar bunkasawa tare da raya al’adun muslunci ne suka dauki nauyin shirya gudanar da wannan shirin bayar da horo.
Gudanar da wani shiri na bayar da horo kan rubutun musulunci da kyautata shi a birnin Islamabad fadar mulkin kasar Pakistan, ya zo ne daidai da lokacin gudanar da bukukuwan maulidin manzon Allah (SAW).
750182
captcha