IQNA

An Buga Tare Da Yada Wani Littafin Mai Suna Musulunci Da Hakkin Dan Adam

19:24 - February 23, 2011
Lambar Labari: 2085542
Bangaren kasa da kasa, An buga tare da yada littafi mai suna musulunci da hakkokin dan adam, wanda kwamitin kare hakkin bil adama na kasar katar tare da hadin gwiwa da cibiyar yada al'adun muslunci ta kasar suka dauki nauyin buga da kuma fitar da shi a kasuwa a birnin Doha.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarata cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na peninsula an bayyana cewa, an buga tare da yada littafi mai suna musulunci da hakkokin dan adam, wanda kwamitin kare hakkin bil adama na kasar katar tare da hadin gwiwa da cibiyar yada al'adun muslunci ta kasar suka dauki nauyin buga da kuma fitar da shi a kasuwa a birnin Doha fadar mulkin kasar Qatar.

Wannan littafi ya kunshi ayoyin kur'ani da dama da kuma hadisan ma'aiki tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iayalan gidansa, wadanda suke nuni da matsayin addinin muslunci kan hakkoki na mutum a rayuwa ta zamantakewa da dai sauransu, kamar yadda ya kawo wasu daga cikin bayanai kan al'adun muslunci da yadda musulunci ke kallon sauran addinai.

Buga tare da yada littafi mai suna musulunci da hakkokin dan adam, wanda kwamitin kare hakkin bil adama na kasar katar tare da hadin gwiwa da cibiyar yada al'adun muslunci ta kasar suka dauki nauyin buga da kuma fitar da shi a kasuwa a birnin Doha, zai taimaka wajen kara wayar da kan masu karkatattar fahimta kan musulunci.

752026


captcha