IQNA

Kungiyar Hadin Kan Musulmi Ta Yi Allah Wadai Da Danne Masu Zanga-zanga A Libiya

14:02 - February 24, 2011
Lambar Labari: 2085771
Bangaren kasa da kasa: kungiyar hadin kan kasashen musulmi a cikin fata sanarwa da ta fitar ta yi Allah wadai da tfin Allah tsine kan gwamnatin kama karya da dannniya ta Libya ke kokarin ta murkushe masu zanga-zanga da karfin tuwo ta hanyar yin kisan kiya da tursasa tsoro a zukatan masu zanga-zangar gami da kawo rarrabuwa a tsakaninsu.


Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; kungiyar hadin kan kasashen musulmi a cikin fata sanarwa da ta fitar ta yi Allah wadai da tfin Allah tsine kan gwamnatin kama karya da dannniya ta Libya ke kokarin ta murkushe masu zanga-zanga da karfin tuwo ta hanyar yin kisan kiya da tursasa tsoro a zukatan masu zanga-zangar gami da kawo rarrabuwa a tsakaninsu.Kamfanin dillancin labaran kur'ani ikna ne ya nakalto daga jaridar Alyaumul Sab'in da ake buga ta a kasar Masar cewa Ikmalul Dine Ihsan Uhlo babban sakataren kungiyar hadin kan kasashen musulmi bayan yin Allah wadai da babbar murya kan kisan kare dangin da ake yi wa masu zanga-zanga da gwmantin kama karya ta Khadafi ke yi ya ce abin day a faru a baya-bayan nan kisan kare dangi ne kan bil adama.


752358
captcha