IQNA

Taron Kasa Da Kasa Kan Fasahar Musulunci A Zamanin Yau A Kasar Holland

10:23 - February 27, 2011
Lambar Labari: 2086960
Bangaren kasa da kasa, Ana shirin gudanar da wani taro a matsayi na kasa da kasa kan fasahar Musulunci a tarihi da kuma matsayinta zamanin yau wanda za agudanar a birnin Amstardam fadar mulkin kasar Holland.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga safin sadarwa na yanar gizo na hum.leiden an bayyana cewa, Ana shirin gudanar da wani taro a matsayi na kasa da kasa kan fasahar Musulunci a tarihi da kuma matsayinta zamanin yau wanda za agudanar a birnin Amstardam fadar mulkin kasar Holland a karon farko.

Cibiyar gudanar da bincike da nazari kan addinin muslunci da ilmomi gami da ala'adunsa da ke jami'ar NISIS ne ya dauki nauyin shirya gudanar da zaman taron a cikin wata mai kamawa, tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasar da kuma wasu kasashen ketrae.

Daga cikin muhimman abubuwan da zaman zai mayar da hankali kansu hard a tarihin al'adu a cikin addinin muslunci, da kuma gagagrumin tasirin da suka yi wajen yaduwar addinin a cikin yankuna na duniya har ya zuwa lokcin yau, da kuma a'adun Musulunci a wannan zamani.

Gudanar da tarona matsayi na kasa da kasa kan fasahar Musulunci a tarihi da kuma matsayinta zamanin yau wanda za agudanar a birnin Amstardam fadar mulkin kasar Holland, zai taimaka wajen kara wayar da kan masu nazari kan muslunci a jami'oin turai.

753675




captcha