IQNA

Taron Kara Wa Juna Sani Kan Ilimin sanin Halayyar Dan Adam A Mahangar Musulunci

10:24 - February 27, 2011
Lambar Labari: 2086962
Bangaren kasa da kasa, An gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan matsayi da kuma mahangar addinin mulunci kan ilimin sanin halayyar dan adam a jami'ar mensota ta kasar Amurka.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na wqow an bayyana cewa, a gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani kan matsayi da kuma mahangar addinin mulunci kan ilimin sanin halayyar dan adam a jami'ar mensota ta kasar Amurka, da nufi kara wayar da kan masu nazari a kasar kan matsayin addinin muslunci da kuma rawar da ya taka a wannan fage.

Bayanin ya ci gaba da cewa wadanda suka shirya gudanar da wannan zaman taro sun yi hakan ne da nufin kara fito da matsayin addinin muslunci kan lamurra da dama dab a asani ba, ko kuma wasu ke zaton muslunci bai san da zamansu a cikin ilmominsa da ka'idojinsa.

Taron dai ya samu halartar masana daga daga wannan jami'a da kuma sauran jami'oi da cibiyoyin bincie daban-daban daga cikin kasar Amurka, inda wasunsu ma suka gabatar da laccoci da mauduai daban-daban da suka shafi ilimin hallayar dan adam.

Zaman taron karawa juna sani kan matsayi da kuma mahangar addinin mulunci kan ilimin sanin halayyar dan adam a jami'ar mensota ta kasar Amurka, na da matukar muhimmanci ta fuskokin ilimi da bincike.

753651




captcha