IQNA

Za A Bude Wani Taro Na Bayar Da Horo Kan Kyautata Rubutun Musulunci A Pakistan

13:12 - February 28, 2011
Lambar Labari: 2087488
Bangaren kasa da kasa, An bude wani taro na bayar da horo kan rubutun Musulunci a cibiyar bunkasa harkokin fasaha ta kasa da ke birnin Islambad fadar mulkin kasar Pakistan, tare da halartar masana daga sassa na kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar News an bayyana cewa, an bude wani taro na bayar da horo kan rubutun Musulunci a cibiyar bunkasa harkokin fasaha ta kasa da ke birnin Islambad fadar mulkin kasar Pakistan, tare da halartar masana daga sassa na kasar ta Pakistan.

Bayanin ya ci gaba da cewa za a fara gudanar da shirin tare da hadin gwiwa da kwamitin raya ala'dun muslunci na PNCA, da kuma ma'aikatar bunkasa harkokin a;adu na Musulunci a kasar, inda dukkanin banagarorin biyu za su bayar da gagagrumar gudunmawa domin ganin shirin ya cimma nasara.

Bude taron na bayar da horo kan rubutun Musulunci a cibiyar bunkasa harkokin fasaha ta kasa da ke birnin Islambad fadar mulkin kasar Pakistan, tare da halartar masana daga sassa na kasar, na da matukar muhimmanci ga masu sha'awar koyon irin wannan fasaha ta Musulunci.

754440



captcha