Kamfanin dillancin labarai na ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne bayan nakaltowa daga jaridar Alintikad ta kasar Labanon ya watsa rahoton cewa; Kungiyar Tauhidin Islami a kasar Labanon ta fitar da wani bayani da ta bukaci kungiyar hadin kan larabawa da ta shiga gadangadan na ganin ta kawo karshen kiyashin da akae yiwa fararen hula masu zanga-zanga da zubar da jininsu a kasar Libya.Bayanin ya kara da cewa al'ummar kasar libya da kuma illahirin sauran al'ummomin kasashen larabawa da musulmi nada hakkin bayyana rayoyinsu da zaluncin da ake yi masu kuma suna da hakkin rayuwa kamar kowa a duniya.
754475