IQNA

‘Yan Kasar China Da Ke Zaune A Malazia Na Shirin Gina Wabi Babban Masallci

13:13 - March 02, 2011
Lambar Labari: 2089277
Bangaren kasa da kasa, ‘yan kasar China da ke zaune akasar Malazia suna shirin gina wani katafaren masallaci a cikin birnin Kualalampour fadar mulkin kasar, da zai zama mallakin kungiyar canawa mazauna kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Thestar an bayyan acewa, ‘yan kasar China da ke zaune akasar Malazia suna shirin gina wani katafaren masallaci a cikin birnin Kualalampour fadar mulkin kasar, da zai zama mallakin kungiyar canawa mazauna kasar ta Malazia, ta yadda hakan zai ba su damar gudanar da harkokinsu na addini tare da junansu a wuri guda.
Bayanin ya ci gaba da cewa babbar kungiyar ‘yan kasar China a kasar Malazia MACMA ita ce za ta dauki nauyin gudanar da aikin ginin masallacin, wanda za a yi shi da salo namusamman da ke nuna al’adun muslunci na kasar China, inda za a bude shi tare da halartar dukkanin musulmmi da suka hada da na China da na malazia.
‘yan kasar China da ke zaune akasar Malazia suna shirin gina wani katafaren masallaci a cikin birnin Kualalampour fadar mulkin kasar, da zai zama mallakin kungiyar canawa mazauna kasar.
755951



captcha