Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar rasid an bayyana cewa, an gudanar da wata zanga-zangar neman sauyi a jiya juma'a a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiyya, duk kuwa da barazanar da mahukuntar kasar suka yi kan shiga kafar wando daya da duk wanda ya gudanar da wani gangami a kasar.
Rahotanni daga kasar ta Saudiyya sun tabbatar da cewa wadanda suka gudanar da zanga-zangar a birnin Riyad, sun yi ta rera taken neman gudanar da sauye-sauye a cikin harkokin mulkin kasar, daga ciki kuwa har da gudanar da zaben 'yan majalisa bisa tsari na demokradiya, maimakon tsarin da akasar take tafiya a kansa, inda sarki shi ne ke ayyana 'yan majalisa da kansa, kuma shi ne ke da iko a kan kundin tsarin mulki.
Hakan na kuma masu zanga-zangar sun bukaci da a saki fursunonin siyasa da mahukuntan kasar ta Saudiyya suke tsare da su tsawon shekaru, ba tare da an gurfanar da su a gaban kuliya ba.
757505