Bangaren kasa da kasa, ma'aikatar kula da harkokin addinin Musulunci a yankin palastinu ta yi Allawadai tare da kakkausar suka kan harin ta'addancin da sojin yahudawan sahyuniya suka kai kan masallacin annabi Yunus da ke garin Halhul.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na alkausar an bayyana cewa, ma'aikatar kula da harkokin addinin Musulunci a yankin palastinu ta yi Allawadai tare da kakkausar suka kan harin ta'addancin da sojin yahudawan sahyuniya suka kai kan masallacin annabi Yunus da ke garin Halhul da ke arewacin garin Alkhalil a gabar yamma da kogin Jordan.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan hari da yahudawan sahyuniya suka kai kan wannan wuri mai tsarki, ya zo a ci gaba da ayyukan tsokana da yahudawan sahyuniyan suke aiwatarwa, wanda ke ci gaba da fuskantar kakkausar daga dukkanin al'ummar palastiu masu lamiri.
ma'aikatar kula da harkokin addinin Musulunci a yankin palastinu ta yi Allawadai tare da kakkausar suka kan harin ta'addancin da sojin yahudawan sahyuniya suka kai kan masallacin annabi Yunus da ke garin Halhul.
757486