Bangaren kasa da kasa, Mabiya addinin muslunci a yankunan arewacin Amurka, sun jaddda wajabcin kara zage dantse wajen yada manufofin da koyarwar addinin musulunci a yankunan, tare da yin aikin da koyarwar kur’ani a cikin rayuwar zamantakewa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nation an bayyana cewa, Mabiya addinin muslunci a yankunan arewacin Amurka, sun jaddda wajabcin kara zage dantse wajen yada manufofin da koyarwar addinin musulunci a yankunan, tare da yin aikin da koyarwar kur’ani a cikin rayuwar zamantakewa a tsakaninsu da sauran al’ummomi.
Bayanin ya ci gaba da cewa daya daga jagororin mabiya addnin musulunci a yankin Sayyid Muhammad sa’id ya bayyana cewa, babban abin da yake gaban mabiya addinin musulunci da ke yankin shi ne yin aiki da koyarwar manzon tsira da kuma sakon kur’ani mai tsarki da ya zo da shi.
Mabiya addinin muslunci a yankunan arewacin Amurka, sun jaddda wajabcin kara zage dantse wajen yada manufofin da koyarwar addinin musulunci a yankunan, tare da yin aikin da koyarwar kur’ani a cikin rayuwar zamantakewa.
757922