Bangaren kasa da kasa, Babban kwamitin kula da harkokin musulmi na kasar Jamus ya nuna matukar damuwa dangane da yadda wasu suke nuna matukar gaba da kyamar addinin musulunci a kasar, musamman ma daga cikin jami’an gwamnati wadanda ya kamata su zama masu kare hakkokin al’ummomin kasarsu.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na nasij an bayyana cewa, Babban kwamitin kula da harkokin musulmi na kasar Jamus ya nuna matukar damuwa dangane da yadda wasu suke nuna matukar gaba da kyamar addinin musulunci a kasar, musamman ma daga cikin jami’an gwamnati wadanda ya kamata su zama masu kare hakkokin al’ummomin kasarsu da suka hada mabiya addinai daban-daban.
A cikin bayanin da kwamitin ya fitar ya yi ishara da furucin da ya fito daga bakin sabon ministan harkokin cikin gidan kasar ta Jamus Hans Peter, da ke cewa addinin muslunci ba ya da wata danganta da kasar Jamus ta fuskacin tarihi, wanda hakan a zahiri na nuna matukar gaba da addinin musulunci da wannan mutum yake da ita.
Babban kwamitin kula da harkokin musulmi na kasar Jamus ya nuna matukar damuwa dangane da yadda wasu suke nuna matukar gaba da kyamar addinin musulunci a kasar, musamman ma daga cikin jami’an gwamnati wadanda ya kamata su zama masu kare hakkokin al’ummomin kasarsu.
760802