Bangaren kasa da kasa, Allah ya yi wa sheikh Umar faruk daya daga cikin fitattun malaman tafsirin kur’ani mai tsarki na kasar Somalia rasuwa a wani asibiti da ke garin Jidda a kasar Saudiyya, bayan fama da rashin lafiya, ya rasu yana da shekaru 71 a duniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin yanar gizo na somali yaum cewa, Allah ya yi wa sheikh Umar faruk daya daga cikin fitattun malaman tafsirin kur’ani mai tsarki na kasar Somalia rasuwa a wani asibiti da ke garin Jidda a kasar Saudiyya, bayan fama da rashin lafiya, ya rasu yana da shekaru saba’in da daya.
Malamin ya shahara tsakanin malaman tafsirin kur’ani mai tsarki a kasar Somalia, an haife shi ne a garin Irmalah da ke yammacin kasar Somalia a cikin shekara a ta 1940, mahaifinsa daya ne daga cikin manyan malaman kasar, kuma ya rasa mahaifansa duka a lokacin da yake da shekaru shida 6 a duniya.
Sheikh Umar faruk daya daga cikin fitattun malaman tafsirin kur’ani mai tsarki na kasar Somalia ya rasu ne a wani asibiti da ke garin Jidda a kasar Saudiyya, bayan fama da rashin lafiya, ya rasu yana da shekaru 71 a duniya, danginsa masu addini ne kuma ya tashi a cikin tarbiyar musulunci.
760696