Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zama na kasa da kasa kan irin gudunmawar da Imam Musa Sadr ya bayar wajen gina al’umma, tare da farkar da ita daga barcin gafala da dimuwa da ta shiga, wanda zai fara ayyukansa daga yau a birnin Tehhran.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kwamitin shirya taruka na kasa da kasa cewa, za a gudanar da wani zama na kasa da kasa kan irin gudunmawar da Imam Musa Sadr ya bayar wajen gina al’umma, tare da farkar da ita daga barcin gafala da dimuwa da ta shiga, wanda zai fara ayyukansa daga yau a birnin Tehran fadar mulkin jamhuriyar musulunci.
Bayanin ya ci gaba da cewa za afara gudanar da zaman taron ne a babban dakin taruka da ke dabndalin hafte tir a kudancin birnin Tehhran, tare da halartar masana daga sassa daban-daban na kasashen musulmi da na larabawa, da wasu daga cikin kasashen nahiyar Asia da kuma Afirka.
za a gudanar da wani zama na kasa da kasa kan irin gudunmawar da Imam Musa Sadr ya bayar wajen gina al’umma, tare da farkar da ita daga barcin gafala da dimuwa da ta shiga, wanda zai fara ayyukansa daga yau a birnin Tehhran.
761821