Bangaren kasa da kasa, shugaban kasar kazakistan a cikin wani jawabi da ya gabatar da ya baiwa al’ummar kasar mamaki, ya nuna rashin gamsuwarsa da saka hijabin musulunci da mata musulmi suke yi a kasarsa, lamarin da ya fuskanci kakausar suka da mayar da martani daga al’ummar kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kafafaen yada labaran kasar Kazagistan an habarta cewa, shugaban kasar ta kazakistan Nur Sultan a cikin wani jawabi da ya gabatar da ya baiwa al’ummar kasar mamaki, ya nuna rashin gamsuwarsa da saka hijabin musulunci da mata musulmi suke yi a kasarsa, lamarin da ya fuskanci kakausar suka da mayar da martani daga al’ummar kasar, musamman ma malaman addidinin muslunci da kuma masana.
Kasar Kazakistan dai daya ce daga cikin kasashen da suka balle daga tsohuwar tarayyar Soviet, inda take da musulmi da yawa, bil hasali ma akasarin mutanen kasar mabiya addinin muslunci, kuma duk da kasantuwar kasar a cikin tarayyar soveit a wancan lokacin da take karkashin akidar gurguzu, mutane suna kallon kansu a matsayin musulmi.
shugaban kasar kazakistan a cikin wani jawabi da ya gabatar da ya baiwa al’ummar kasar mamaki, ya nuna rashin gamsuwarsa da saka hijabin musulunci da mata musulmi suke yi a kasarsa, lamarin da ya fuskanci kakausar suka da mayar da martani daga al’ummar kasar.
762652