Bangaren kasa da kasa, kungiyar hadin kan kasashenmusulmi ta OIC ta sanar cewa ta bude wasu kwamitoci na bayar da taimakon gaggawa ga mutanen birnin Bungazi na kasar Libya, sakamakon mawuyacin halin da suka samu kansu a ciki na hare-hare da magoya bayan Gaddafi.
Kamfanin dillancin labaran kur'ani na iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-dastur an bayyana cewa, kungiyar hadin kan kasashenmusulmi ta OIC ta sanar cewa ta bude wasu kwamitoci na bayar da taimakon gaggawa ga mutanen birnin Bungazi na kasar Libya, sakamakon mawuyacin halin da suka samu kansu a ciki na hare-hare da magoya bayan shugaban mulkin kama karya na kasar.
Bayanin ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai dubban mutane da suke bukatar taimakon gagagwa wadanda suka rasa gidajensu da 'yan uwansu da iayalansu, sakamakon halin da kasar ta samu kanta a ciki, wanda hakan ya tilasta dukkanin bangarori da suke cikin kungiyar tattauna hanyoyin kai taimako ga muten birnin na Bingazi.
Kungiyar hadin kan kasashenmusulmi ta OIC ta sanar cewa ta bude wasu kwamitoci na bayar da taimakon gaggawa ga mutanen birnin Bungazi na kasar Libya, sakamakon mawuyacin halin da suka samu kansu a ciki na hare-hare da magoya bayan Gaddafi.
763514