Bangaren kasa da kasa, kwamitin kula da harkokin addinin Musulunci na kasar Amurka ya bukaci mahukuntar kasar da su dauki matakin gudanar da bincike kan yadda wasu 'yan tsiraru suke wulakanta kur'ani mai tsarki a kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na PRNews cewa, kwamitin kula da harkokin addinin Musulunci na kasar Amurka ya bukaci mahukuntar kasar da su dauki matakin gudanar da bincike kan yadda wasu 'yan tsiraru suke wulakanta kur'ani mai tsarki a kasar, wanda ya fuskanci kakkausar suka daga sassa daban-daban na kasashen duniya.
A cikin shekarar da ta gabata ne wani daya daga cikin masu kiran kansu malaman mabiya addinin kirista a kasar Amurka ya sanar da ranar sha daya ga watan satumba a matsayin ranar kone kur'ani mai tsarki da cin zarafin addinin musulunc, bayan da ya danganta littafin mai tsarki munan abubuwa.
kwamitin kula da harkokin addinin Musulunci na kasar Amurka ya bukaci mahukuntar kasar da su dauki matakin gudanar da bincike kan yadda wasu 'yan tsiraru suke wulakanta kur'ani mai tsarki a kasar.
763024