Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tayyar cewa, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta kasar Lebanon Hizbullah ta yi kakkausar suka kan yadda mahukuntan kasar Bahrain suka dauki wani sabon salon a murkushe masu zanga-zangar lumana a kasar domin gudanar da sauye-sauye na siyasa, da za su baiwa kowane bangare damar shiga a dama da shi a cikin harkokin siyasar kasar.
A ranakun Asabar da Lahadi da suka gabata, jami'an tsaron kasar Bahrain tare da 'yan bangar gwamnati sun sake afkawa kan fararen hula masu gudanar da zanga-zangar lumana, inda suka kashe akalla mutum daya tare da jikkata daruruwa, lamarin da ya sanya gamayyar kungiyoyin kwadagon kasar kiran yaji aiki na kasa baki daya, inda a jiya aka rufe dukkanin makarantu da kamfanoni da wuraren ayyukan gwamnati da na jama'a a fadin kasar.
Jam'iyun siyasa gami da kungiyoyin lauyoyi da kuma na farar hula, da ma wasu da dama daga cikin malaman addinin Musulunci na kasar ta Bahrain, sun yi kakkausar suka kan shigar shugula da mahukuntan kasar Saudiyya suke yi a cikin harkokin kasarsu, tare da bayyana aikewa da sojojin da Saudiyya ta yi jiya Lahadi zuwa kasar Bahrain da cewa, daidai yake mamayar kasar da kuma shelanta yaki kan al'ummar kasar ta Bahrain, a kan haka duk abin da ya faru a kasar, mahukuntan Saudiyya da na Bahrain suke da alhakinsa.
763503