Bangaren kasa da kasa, An kafa wani kwalejin nazari kan harkokin tattalin arzikin Musulunci a kasar Belgium, wanda cibiyoyi goma sha biyar suka hada gwiwa wajen kafawa da nufin kara bunkasa harkokin nazari da binike kan tattalin arziki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo Trend.rnews cewa, an kafa wani kwalejin nazari kan harkokin tattalin arzikin Musulunci a kasar Belgium, wanda cibiyoyi goma sha biyar suka hada gwiwa wajen kafawa da nufin kara bunkasa harkokin nazari da binike kan tattalin arziki a mahangar addinin Musulunci.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan kwaleji ya hada masana kan harkokin tattalin arziki da suke da cikkaiyar masana kan harkokin kudi da kasuwanci a mahangar Musulunci, wadanda su ne za su taiamaka masu nazari da bincike a wannan kwaleji, wanda yanzu haka ya fara gudanar da ayyukansa.
An kafa wani kwalejin nazari kan harkokin tattalin arzikin Musulunci a kasar Belgium, wanda cibiyoyi goma sha biyar suka hada gwiwa wajen kafawa da nufin kara bunkasa harkokin nazari da binike kan tattalin arziki.
763913