IQNA

An Fara Rijistar Sunayen Masu Gasar Karatun Kur'ani Ta Tartil A Kasar UAE

18:35 - March 17, 2011
Lambar Labari: 2097312
Bangaren kasa da kasa, An fara gudanar da rijistar sunayen masu gasar karatun kur'ani mai tsarki ta tartil a kasar hadaddiyar daular larabawa, wanda kuma shi ne karo na biyar da za a gudanar da irin wannan gasa a kasar tare da halartar wasu daga cikin malaman kur'ani na kasar da jami'an gwamnati.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar al-bayan an bayyana cewa, An fara gudanar da rijistar sunayen masu gasar karatun kur'ani mai tsarki ta tartil a kasar hadaddiyar daular larabawa, wanda kuma shi ne karo na biyar da za a gudanar da irin wannan gasa a kasar tare da halartar wasu daga cikin malaman kur'ani na kasar da jami'an gwamnati.

Wannan gasa na daga cikin irinta da makaranta kur'ani na kasar hadaddiyar daular larabawa suka saba gudanarwa tun kimanin shekaru biyar da suk agabata, wadda ke samun halartar matasa 'yan kasa da shekaru ashirin da biyar, cibiyar kula da ayyukan gasar karatu da hardar kur'ani mai tsarki ta kasar ce ta dauki nauyin shirya wannan babbar gasa.

An fara gudanar da rijistar sunayen masu gasar karatun kur'ani mai tsarki ta tartil a kasar hadaddiyar daular larabawa, wanda kuma shi ne karo na biyar da za a gudanar da irin wannan gasa a kasar tare da halartar wasu daga cikin malaman kur'ani na kasar da jami'an gwamnati.

764889

captcha