IQNA

An Yi KIra Ga Malaman Musulunci Da Su Daina Yin Shiru Kan Kisan Mutanen Bahrain

18:15 - March 19, 2011
Lambar Labari: 2097592
Bangaren siyasa da zamantakewa, daya daga cikin manayan malaman addinin Musulunci da ake komawa zuwa gare su a jamhuriyar Musulunci Ayatollah Ozma Muhammad Alawi Gorgani ya bayyana cewa, dole malamai su safke nauyin da rataya kansu wajen kalubalantar matakin kashe mutane a Bahrain.



Kamfanin dilalncin labaran iqa ya habarat cewa, a wani rahoto da ya nakalto daga bangaren yada labaransa na birnin Qom an bayyana cewa, daya daga cikin manayan malaman addinin Musulunci da ake komawa zuwa gare su a jamhuriyar Musulunci Ayatollah Ozma Muhammad Alawi Gorgani ya bayyana cewa, dole malamai su safke nauyin da rataya kansu wajen kalubalantar matakin kashe mutane a Bahrain, wanda jami'an tsaron kasar da soojojin kasashen larabawa suke yi ba ji ba gani.

Bayanin ya ci gaba da cewa wannan na daya daga cikin irin bayanan yin Allawadai da manyan malaman addinin Musulunci na kasar Iran suka fitar a cikin 'yan lokutan nan da al'ummar musulmi na kasar Bahrain suke ganin kisan gilla daga sarakunan larabawan kasashen tekunfasha.

Daya daga cikin manayan malaman addinin Musulunci da ake komawa zuwa gare su a jamhuriyar Musulunci Ayatollah Ozma Muhammad Alawi Gorgani ya bayyana cewa, dole malamai su safke nauyin da rataya kansu wajen kalubalantar matakin kashe mutane a Bahrain.

765382



captcha