IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta OIC Ta Yi Allawadai Da Ta'addancin Isra'ila A Palastinu

20:26 - March 27, 2011
Lambar Labari: 2098378
Bangaren kasa da kasa, babban sakataen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ya yi kakkausar suka dangane da matakan wuce gonad a iri da zalunci da haramtacciyar kasar Isra'ila take dauka kan al'ummar palastinu marassa kariya.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, Babban sakataen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ya yi kakkausar suka dangane da matakan wuce gonad a iri da zalunci da haramtacciyar kasar Isra'ila take dauka kan al'ummar palastinu marassa kariya a cikin kwanakin nan musamman ma a yankin zirin Gaza.

A cikin wani byani da ya fitar bababn sakataren kungiyar ya bayyana irin wadannan ayyuka na ta'addanci da gwamnatin yahudawan sahyuniyan take aikatawa kan fararen hula palastinawa da cewa aiki ne da ya yi hannaun riga da dukaknin ka'idoji da kuma dokoki na kasa da kasa, a akn ya kirayi dukkanin gwamnatoci masu fada a ji da suke safke nauyin da ya rataya kansu.

Babban sakataen kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta OIC ya yi kakkausar suka dangane da matakan wuce gonad a iri da zalunci da haramtacciyar kasar Isra'ila take dauka kan al'ummar palastinu marassa kariya a cikin yankunan Gaza da kuma gabar amma da kogin Jordan.

766201



captcha