Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; musulmi a garin Lakhunu a jiya lakwas ga watan farvardin shekara ta dubu daya da dari uku da tisi'in hijira shamsiya sun gudanar da wata zanga-zangar lumana da a ciki suka fito fili suka nuna adawa da takaici da kuma Allah wadai da yadda ake yi wa al'ummar kasar Bahrain kisan kiyashi.Wannan zanga-zangar hukumar tabbatar da sulhu ce ta shirya kuma a jawabin da hujjatul Islam Said Amir Haidar Radawi ya bayyana cewa; Amerika ita babbar makiyin musulmi kuma a yau ya zama wajibi kuma dole musulmi su magance sabani da bambance-bambancen da ke tsakaninsu don haka ya bas u dama baki daya murkushe zalunci.
766628