Bangaren kasa da kasa, Ana shirin fara gudanar da wani zaman taro domin yin nazari kan ilmomin kur’ani da kuma addnin musulunci a jami’ar Oxford ta kasar Birtaniya, da nufin kara fadada fahimta da bincike kan wannan addinin da koyarwa kamar yadda yake a cikin koyarwarsa.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na quran instute an bayyana cewa, ana shirin fara gudanar da wani zaman taro domin yin nazari kan ilmomin kur’ani da kuma addnin musulunci a jami’ar Oxford ta kasar Birtaniya, da nufin kara fadada fahimta da bincike kan wannan addinin da koyarwa kamar yadda yake a cikin koyarwarsa, maimakon saurare daga wadanda ba musulmi ba kan addinin muslunci.
A bangare guda kuma za a gudanar da wani zaman taro na karawa juna sani a babban dakin gudanar da taruka na jami’ar Haward a kasar Amurka, tare da halartar masana daga sassan kasar, wanda babbar cibiyar kula da ayyukan addinin musulunci ta kasar ta dauki nauyinshiryawa da gudanarwa da nufin kara masaniya ga wadanda suke son yin nazari ko samun karin haske kan addinin muslunci ga dukkanin al’ummomin duniya baki daya.
An fara gudanar da wani zaman taro domin yin nazari kan ilmomin kur’ani da kuma addnin musulunci a jami’ar Oxford ta kasar Birtaniya, da nufin kara fadada fahimta da bincike kan wannan addinin da koyarwa kamar yadda yake a cikin koyarwarsa ga alummomi.
769071