IQNA

Ana Shirin Fara Gudanar Da Wani Zaman Taro Kan Dokokin Musulunci A Malazia

14:35 - April 07, 2011
Lambar Labari: 2102007
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro na tattaunawa kan shari'ar addinin muslunci da kuma dokokin da ta tabbatar da su, wanda zai gudana abirnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia tare da halartar masana na ciki da kasashen ketare.


Kamfanin dillanicn labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Bernama an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro na tattaunawa kan shari'ar addinin muslunci da kuma dokokin da ta tabbatar da su, wanda zai gudana abirnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia tare da halartar masana na ciki da kasashen ketare musamman ma daga kasashen musulmi da na larabawa.

Bayanin ya ci gaba da cewa zaman taro zai yi dubi ne kan muhimman abubuwa da shari'ar muslunci ta mayar da hankali kansu, wanda kuma addinin Musulunci yana kallon rayuwa baki dayanta a matsayin wata aba da take cikin tsari da mahaliccin kowa da komi ya tsara, wanda kuma hakan shi ne abin da dukkanin musulmi suka yi imani da shi.

Za a gudanar da wani zaman taro na tattaunawa kan shari'ar addinin muslunci da kuma dokokin da ta tabbatar da su, wanda zai gudana abirnin Kualalampour fadar mulkin kasar Malazia tare da halartar masana na ciki da kasashen waje.

769884



captcha