IQNA

16:54 - April 10, 2011
Lambar Labari: 2103496
Bangaren kasa da kasa, mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah sun gunar da gangami a sassa daban-daban na kasar domin nuna rashin amincewa da matakan zalunci da danniya da mahukuntan kasar suke dauke domin murkushe masu neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a cikin harkokin kasar.
Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Rasid an bayyana cewa, mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah sun gunar da gangami a sassa daban-daban na kasar domin nuna rashin amincewa da matakan zalunci da danniya da mahukuntan kasar suke dauke domin murkushe masu neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a cikin harkokin mulimin kasar.
Bayanin ya ci gab ada cewa gungun matasan ya nuna rashin amincewa da matakan da mahukuntan kasar suke dauka na yin amfani da karfi wajen murkushe duk wata zanga-zanga ta neman sauye-sauye na siyasa akasar, inda suka hada baki da mahukuntan gidan sarautar ali saud na kasar Saudiyya domin murkushe yunkurin al’ummar Bahrain, suka ce wannan zalunci ne karara.
Matasan kasarBahrain da suke bore sun sakawa ranar Asabar da ta gabata ranar ‘yanci sun kuma nemi masu rayayyen lamiri daga cikin mutanen kasar da su taru a dandalin shahidai da ke tsakiyar bin Manama fadar mulkin kasar, domin nuna rashin amincewarsu da zalunci sarakunan kasar.
mabiya mazhabar iyalan gidan manzon Allah sun gunar da gangami a sassa daban-daban na kasar domin nuna rashin amincewa da matakan zalunci da danniya da mahukuntan kasar suke dauke domin murkushe masu neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa.
770798


Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: