IQNA

Jami’ar Azhar Ta Mayar Da Martani Kan Keta Alfarmar Kur’ani Mai Tsarki

16:23 - April 12, 2011
Lambar Labari: 2104807
Bangaren kasa da kasa, babbar kungiyar malaman addini na jami’ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ta fitar da wani bayani da ke yin kakkausar suka kan keta alfarmar kur’ani mai tsarki da wasu la’anannu suka yi a kasar Amurka da suna ‘yancin fadar albarkacin baki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto rahoto daga shafin sadarwa na yanar gizo na muhit cewa babbar kungiyar malaman addini na jami’ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ta fitar da wani bayani da ke yin kakkausar suka kan keta alfarmar kur’ani mai tsarki da wasu la’anannu suka yi a kasar Amurka da suna ‘yancin fadar albarkacin baki, da hakan ya hada hakoron tunzura mabiya wasu addinai kan addinin musulunci da mabiyansa.
An gudanar da zanga-zanga da dubban daruruwan mutane suka shiga a cikin kasashen musulmi daban-daban domin yin allawadai da dukkanin wadanda suke d ahannu wajen aikata wannan mummnan aiki, wanda ya yi hannun riga da dukkanin koyarwar addinai na duniya.
Al'ummomin musulmi daga sassa daban-daban na duniya suna ci gaba da nuna fushinsu dangane da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu masu kiran kansu malaman kiristanci suka yi a cikin kasar Amurka a cikin wannan mako.
772275


captcha