IQNA

Mahukuntan Kasar Bahrain Na Hankoron Tayar Da Fitinar Mazhaba A Cikin Kasar

16:27 - April 18, 2011
Lambar Labari: 2107873
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Bahrain Nabil Rajab ya bayyana cewa, gidan sarautar kasar ta Bahrain na kokarin tayar da fitinar mazhaba a cikin kasar, da nufin kawar da hankulan al’ummomin duniya kan barnar da suke tafkawa a cikin kasar, suna yin hakan ne kuwa ta hanyar rusa masallatai da wuraren tarukan addini.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Alalam an bayyana cewa, babban sakataren kungiyar kare hakkin bil adama ta kasar Bahrain Nabil Rajab ya bayyana cewa, gidan sarautar kasar ta Bahrain na kokarin tayar da fitinar mazhaba a cikin kasar, da nufin kawar da hankulan al’ummomin duniya kan barnar da suke tafkawa a cikin kasar, suna yin hakan ne kuwa ta hanyar rusa masallatai da wuraren tarukan addini na mabiya mazhabar iyaln gidan manzon Allah masu rinjaye a kasar.
Daya daga cikin manyan malaman addini na kasar Bahrain Abdulkarin Abduljalil ya bayyana cewa, mutanen kasar Bahrain sun mabiya mazhabar shi’a da ‘yan sunna na kasar sun rayu tsawon shekaru a kasar ba tare da wata matsala ba, amma a lokacin da suka fara bore domin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar sai gidana sarauta mayar da maganar ta mazhabanci domin samun damar murkushe masu bore a fadin kasar.
Malamin ya ci gaba da cewa babu wani dalili da zai sanya mahukuntan Bahrain su fake da batun mazhaba domin murkushe masu gudanar da zanga-zangar neman sauyi na siyasa akasar, tare da tabbatar da tsarin kama karya kansu, domin kuwa kowa aduniya ya san abin da ke faruwa ba shi da wata dangantaka da batun mazhaba kamar yadda gidanasarautar da masu kare daga kasashen larabawa suke rayawa.
Al’ummar kasar Bahrain mabiya mazhabar shi’a da ‘yan sunna na kasar sun rayu tsawon shekaru a kasar ba tare da wata matsala ba, amma a lokacin da suka fara bore domin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar sai gidana sarauta mayar da maganar ta mazhabanci domin samun damar murkushe masu zanga-zanga.
775618

captcha