IQNA

Babban Zaman Taron Limaman Masallatai A Fadin Kasar Auzbakistan

16:23 - April 18, 2011
Lambar Labari: 2107876
Bnagaren kasa da kasa, ana ci gaba da gudanar da babban zaman taro na limamaman masallatai na kasar Auzbakistan, tare da halartar malamai daga sassa daban-daban na kasar, da nufin yin bita kan ayyukan da suke gudanarwa na fadarwa a tsaknain al’ummar musulmi na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da ta hada wakilinsa da babban malamin kasar Auzbakistan kuma babban mai bayar da fatawa Artq Bik ya bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da babban zaman taro na limamaman masallatai na kasar Auzbakistan, tare da halartar malamai daga sassa daban-daban na kasar, da nufin yin bita kan ayyukan da suke gudanarwa na fadarwa a tsaknain al’ummar musulmi na kasar baki daya.
Wani labarin kuma ya yi nuni da cewa babbar kungiyar malaman addini na jami’ar Azhar da ke birnin Alkahira na kasar Masar ta fitar da wani bayani da ke yin kakkausar suka kan keta alfarmar kur’ani mai tsarki da wasu la’anannu suka yi a kasar Amurka da suna ‘yancin fadar albarkacin baki, da hakan ya hada hakoron tunzura mabiya wasu addinai kan addinin musulunci da mabiyansa.
An gudanar da zanga-zanga da dubban daruruwan mutane suka shiga a cikin kasashen musulmi daban-daban domin yin allawadai da dukkanin wadanda suke d ahannu wajen aikata wannan mummnan aiki, wanda ya yi hannun riga da dukkanin koyarwar addinai na duniya.
Al'ummomin musulmi daga sassa daban-daban na duniya suna ci gaba da nuna fushinsu dangane da keta alfarmar kur'ani mai tsarki da wasu masu kiran kansu malaman kiristanci suka yi a cikin kasar Amurka a cikin wannan mako.
775588


captcha