Bangaren kasa da kasa, al’ummar musulmi na ci gaba da gudanar da zanga-zangar la’antar mahukuntan kasar Saudiyya na kasar Bahrain sakamakon ci gaba da yin kisan gilla akan al’ummar musulmi na kasar Bahrain da suke yi ba ji ba gani, domin sun bukaci da a gudanar da sauye-sauye na siyasa acikin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar alkausar an bayyana cewa, al’ummar musulmi na ci gaba da gudanar da zanga-zangar la’antar mahukuntan kasar Saudiyya na kasar Bahrain sakamakon ci gaba da yin kisan gilla akan al’ummar musulmi na kasar Bahrain da suke yi ba ji ba gani, domin sun bukaci da a gudanar da sauye-sauye na siyasa a cikin kasar wadda sarakunan alikhalifa suka mamaye komai acikinta.
Babban malamin addini na kasar Bahrain Abdulkarin Abduljalil ya bayyana cewa, mutanen kasar Bahrain sun mabiya mazhabar shi’a da ‘yan sunna na kasar sun rayu tsawon shekaru a kasar ba tare da wata matsala ba, amma a lokacin da suka fara bore domin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar sai gidana sarauta mayar da maganar ta mazhabanci domin samun damar murkushe masu bore a fadin kasar.
Malamin ya ci gaba da cewa babu wani dalili da zai sanya mahukuntan Bahrain su fake da batun mazhaba domin murkushe masu gudanar da zanga-zangar neman sauyi na siyasa akasar, tare da tabbatar da tsarin kama karya kansu, domin kuwa kowa aduniya ya san abin da ke faruwa ba shi da wata dangantaka da batun mazhaba kamar yadda gidanasarautar da masu kare daga kasashen larabawa suke rayawa.
Al’ummar kasar Bahrain sun mabiya mazhabar shi’a da ‘yan sunna na kasar sun rayu tsawon shekaru a kasar ba tare da wata matsala ba, amma a lokacin da suka fara bore domin neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa a kasar sai gidana sarauta mayar da maganar ta mazhabanci domin samun damar murkushe masu zanga-zangar lumana.
775433