IQNA

A Yanke Hukunci Dauri Kwanaki 70 A Kan Wani Da Ya Wulakanta Kur’ani A Birtaniya

14:36 - April 20, 2011
Lambar Labari: 2109194
Bangaren kasa da kasa, kotun kasar Birtaniya ta yanke hukunci dauri kwanaki saba’in a kan wani jami’in tsaron kasar da ya wulakanta kur’ani mai tsarki, da nufin hakan ya zama darasi ga masu hankoron tsokanar mabiya addinin muslunci a kasar ta hanayar wulaknata abubuwansu masu tsarki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo an bayyana cewa, kotun kasar Birtaniya ta yanke hukunci dauri kwanaki saba’in a kan wani jami’in tsaron kasar da ya wulakanta kur’ani mai tsarki, da nufin hakan ya zama darasi ga masu hankoron tsokanar mabiya addinin muslunci a kasar ta hanyar wulaknata abubuwansu masu tsarki, kamar yadda wasu suka dauki irin wannan salo a wasu kasashen nahiyar turai.
Shi dai wannan sojin kasar Birtaniya mai suna Andro Rayan ya sace wani kwafin kur’ani mai tsarki daga wani dakin karatu, inda ya tafi da shi a gaban mutane ya kone shi da wuta, kotun ta ce bisa laifi da aka samu Anro da aikatawa ta yanke masa hukuncin daurin kwanaki saba’in a gidan kaso.
kotun kasar Birtaniya ta yanke hukunci dauri kwanaki saba’in a kan wani jami’in tsaron kasar da ya wulakanta kur’ani mai tsarki, da nufin hakan ya zama darasi ga masu hankoron tsokanar mabiya addinin muslunci a kasar ta hanayar wulaknata abubuwansu masu tsarki.
776963
captcha