Bangaren kasa da kasa, cibiyar yada ilimi da bunkasa al’adun muslunci ta nur za ta dauki nauyin bakuncin wani babban taro na kungiyoyin kasashen musulmi da suke gudanar da ayyukan bunkasa al’adun addinin muslunci, da kuma ilimi a cikin kasashen da ma sauran kasashen ketare.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, cibiyar yada ilimi da bunkasa al’adun muslunci ta nur za ta dauki nauyin bakuncin wani babban taro na kungiyoyin kasashen musulmi da suke gudanar da ayyukan bunkasa al’adun addinin muslunci, da kuma ilimi a cikin kasashen da ma sauran kasashen ketare da suka hada da kasashen da ba na musulmi ba.
A bangare guda kuma an fara gudanar da taron baje koli na kayan fasahar masana a musulunci a kasar Birtaniyam, wanda babbar cibiyar kula da kayan tarihin muslunci ta kasar ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa tun daga makon da ya gabata a babban dakin tarukanta da ke birnin London fadar mulkin kasar.
Taron yana samun halartar masana kan harkokin al’adu da tarihi daga jami’ar birnin London da kuma wasu cibiyoyi na mabiya addinin muslunci da ke cikin sassan kasar, haka nan kuma ana nuna wasu daga cikin abubuwan da aka samar na fasahar musulunci a kasar weadanda suke nuna kokarin masana musulmi masu fasaha da suke gudanar da ayyukansu na al’adu.
777698