Bangaren kasa da kasa, za a raba kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki a birnin Leak city babban birnin jahar Yuta akasar kasar Amurka, wanda babbar majami’ar Protestan za ta dauki nauyin rabawa ga mabiya addinin kirista domin su san abin da ke cikin kur’ani mai tsarki.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na kamfanin dillancin labaran reaters an bayyana cewa za a raba kwafi-kwafi na kur’ani mai tsarki a birnin Leak city babban birnin jahar Yuta akasar kasar Amurka, wanda babbar majami’ar Protestan za ta dauki nauyin rabawa ga mabiya addinin kirista domin su san abin da ke cikin kur’ani mai tsarki, domin kauce wa duk wata rashin fahimta tsakaninsu da musulmi.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nasij kuma an bayyana cewa, za aguudanar da wani zaman taro na kara wa juna sani kan mu’ujizar ilimin kur’ani mia tsarki da kuma sunnar manzon Allah (SAW) wanda za agudanar a karo na goma a birnin Istanbul fadar mulkin kasar Turkiya, tare da halartar masana daga sassa na kasashen duniya, musamman ma daga kasashen larabawa da na musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro an sabar gudanar da shi a kasar ta Turkiya, wanda ma’aikatar kula da ayyukan addinin musuluci ta kasar ta kan dauki nauyin shiryawa da gudanarwa a kowace shekara, tun daga shekara ta dubu biyu da daya da ta gabata, inda masana kan gabatar da laccoci da kuma makalolin da suka tanada kan hakan.
780341