Bangaren kas ada kasa, babban malami kuma mataimakin shugaban majalisar mabiya mazhabar shi’a a kasar Lebanon ayatollah Abdulamir Qabalan ya kirayi mabiya addinan musulunci da kiristanci na kasar Lebanon zuwa ga hadin kai da fahimtar juna a dukkanin bangarorin da suka hada su.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na iloubnan an bayyana cewa, babban malami kuma mataimakin shugaban majalisar mabiya mazhabar shi’a a kasar Lebanon ayatollah Abdulamir Qabalan ya kirayi mabiya addinan musulunci da kiristanci na kasar Lebanon zuwa ga hadin kai da fahimtar juna a dukkanin bangarorin da suka hada su na siyasa da kuma zamantakewa.
Malamin ya yi wannan kira ne a cikin wani sakon taya murna da ya aike wa jagoran mabiya addinin kirista na kasar Lebanon na zagayowar ranar easter, wadda mabiya addinin kirista suke girmamawa, ya kara kda cewa dukkanin addiunan biyu suna tarihin zama tare da fahimtar juna a tsakaninsu, a kan wajibi da ya rataya kan dukkanin mabiyansu a Lebanon sun yi koyi da tarihin addinan biyu.
Babban malami kuma mataimakin shugaban majalisar mabiya mazhabar shi’a a kasar Lebanon ayatollah Abdulamir Qabalan ya kirayi mabiya addinan musulunci da kiristanci na kasar Lebanon zuwa ga hadin kai da fahimtar juna a dukkanin bangarorin da suka hada su a rayuwa.
780346