IQNA

Amurka Ba Ta Amince Da Hukunci Kisa Kan Masu Zanga-Zanga A Bahrain Ba

13:52 - May 01, 2011
Lambar Labari: 2115236
Bangaren kasa da kasa, Amurka ta sanar cewa ba ta amince da hukuncin kisa da wata kotun sojin kasar Bahrain ta yanke kan masu gudanar da zanga-zanga ba, lamarin da ya baiwa al'ummomin duniya mamaki, bisa laka'ari da cewa Bahrain ba isa ta yanke irin wannan hukunci ba tare da amincewar Amurka ba.

Kamfanin dilalcin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga wani shafin yanar gico cewa, Amurka ta sanar cewa ba ta amince da hukuncin kisa da wata kotun sojin kasar Bahrain ta yanke kan masu gudanar da zanga-zanga ba, lamarin da ya baiwa al'ummomin duniya mamaki, bisa laka'ari da cewa Bahrain ba isa ta yanke irin wannan hukunci ba tare da amincewar Amurka ba, da sarakunan wahabiyawan yankin.

A wani labarin kuma makamanicn wannan kungiyar tarayyar turai ta yi kakkausar suka kan hukuncin kisa da kotun sojin kasar Bahrain ta yanke kan wasu matasa da suka shiga zanga-zangar neman sauyi a kasar.
Kakakin kungiyar tarayyar turai Jerzy Buzek, ya fadi jiya cewa ko alama ba za su amince da hukuncin kisan da kotun sojin kasar Bahrain ta yanke kan matasan hudu ba, kuma kungiyar tana yin kira ga mahukuntan kasar ta Bahrain ta kawo karshen yin amfani da karfin da take yi kan fararen hula masu neman a gudanar da sauye-sauyen siyasa a kasar.
A jiya ne wata kotun soji da mahukuntan Bahrain suka kafa cikin makwannin suka, ta yanke hukuncin kisa kan wasu matasa hudu, bisa zargin cewa suna da hannu wajen mutuwar 'yan sanda biyu a lokacin gudanar da zanga-zanga a birnin Manama.
Al'ummomin duniya da dama da suka hada da kungiyoyin kare hakkin bil adama, suna ci gaba da yin Alawadai da mahukuntan kasar Bahrain da kuma na Saudiyya, sakamakon yin amfani da karfin soji da suka yi wajen yin kisan gilla a kan fararen hula masu neman a gudanar da sauye-sauye na siyasa ta hanyar lumamana a cikin kasar ta Bahrain.

783502

captcha