IQNA

Ta'addanci A Bahrain Na Nuni Da Zurfin Kiyayyar Gidan Sarautar Kasar Kan Al'umma

12:50 - May 05, 2011
Lambar Labari: 2117692
Bangaren kasa da kasa; munanan matakai da kai wa fararen hula hari na rashin imani da tausayi da fitar da kuma zartar da hukumcin kisa kan matasa masu zanga-zangar neman sauyi na nuni da yadda shugabanni da gwamnatin fasadi ta Ali Khalifa a kasar da kuma ta Ali Saudiya dad a zurfin kiyayya da nuna karan tsana kan al'ummar wannan kasa ta Bahrain da ake nuna wa zalumci mafi muni a tarihi.


Kamfanin dillacin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa rahoton cewa; munanan matakai da kai wa fararen hula hari na rashin imani da tausayi da fitar da kuma zartar da hukumcin kisa kan matasa masu zanga-zangar neman sauyi na nuni da yadda shugabanni da gwamnatin fasadi ta Ali Khalifa a kasar da kuma ta Ali Saudiya dad a zurfin kiyayya da nuna karan tsana kan al'ummar wannan kasa ta Bahrain da ake nuna wa zalumci mafi muni a tarihi. Abin mamaki da daurin kai matuka yadda gwamnatin Ali Khalifa da kuma Ali Saudiya ke yiwa al'ummar Bahrain kisan kiyashi da kisan mummuke a daidai lokacin da koma na gani da samin masaniyar abubuwan da ke faruwa a wannan kasa musamman a daidai wannan lokaci na sauye-sauye da canji a kasashen larabawa musulmi amma gwamnatin Baharain da gidan sarautar kasar na amfani da karfin da yafi kima da nuna zalunci.

786275
captcha