Bangaren kasa da kasa, cibiyar Nur ta birnin Qom na jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke gudanar da ayyukanta ta fuskacin yada a'adun muslunci ta na'ura mai kwakwalwa ta bayyana cewa a shirye take ta fadada ayyukanta zuwa kasar jamhuriyar Cheque.
Kamfanin dillancin labarn iqna ya habarta cewa, wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Nur an bayyana cewa cibiyar Nur ta birnin Qom na jamhuriyar Musulunci ta Iran da ke gudanar da ayyukanta ta fuskacin yada a'adun muslunci ta na'ura mai kwakwalwa ta bayyana cewa a shirye take ta fadada ayyukanta zuwa kasar jamhuriyar Cheque wadda day ace daga cikin kasashen tarrayar turai.
Babban daraktan cibiyar ya bayyana cewa, jami'an da suka kawo wannan ziyara a cibiyar nur, suna tare da wasu daga cikin manyan jami'a na jamhuriyar muslunci ta Iran, da suka hada da shugaban cibiyar bunkasa harkokin ilimi da al'adun Musulunci, gami da shugaban cibiyar kunsanto da mazhabobin muslunci ta duniya.
Wasu daga cikin fitattun masana da 'yan siyasa a kasar Iraki sun kai ziyara a babbar cibiyar nan ta na'ura mai kwakwalwa da ke birin kum a jamhuriyar Musulunci ta Iran, domin ganewa idanunsu irin ayyukan da suke gudanarwa na bunkasa harkokin ilimi ta wannan hanya ta zamani.
786565