Bangaren kasa da kasa; taron karawa juna sani kan taimakwa al'ummar kasar Libiya da kuma yadda suke tasiri a duniyar musulmi da za a gudanar a ranar ashirin da hudu ga watan Urdebehesht da muke ciki na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal.
Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran Ikna ne ya watsa rahoton cewa; taron karawa juna sani kan taimakwa al'ummar kasar Libiya da kuma yadda suke tasiri a duniyar musulmi da za a gudanar a ranar ashirin da hudu ga watan Urdebehesht da muke ciki na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal.wannan wani taron karawa juna sani da sada zumunta da kuma yin dubin hanyoyin da za a bi a taimakawa al'ummar Libiya a kasar ta Senegal da kuma za a samu halartar kungiyoyi masu yawa na musulmi a kasar ta Senegal.Kuma wadanda suka shirya wannan taron sun tabbatar da halartar masana addinin musulunci da limaman juma'a dam asana harkokin siyasar kasar Senegal inda za su yi nazari kan boren da al'ummar kasar ta Libiya ke ci gaba da yi kan gwamnatin da kuma kisan da ake yi way an tawaye da gwamnatin Kadhafi ke yi da kuma yadda tasirin tashin hankali da rikici a kasar Libiya zai yadu zuwa sauran kasashen afrika da kuma sauran kasashen musulmi.Kuma Haj Mustapha Sice tsowon jakadan kasar Senegal a kasar Masar kuma shugaban kungiyar taimakawa al'ummar Libiya a Senegal ne zai jagoranci wannan taron.
788780