Bangaren kasa da kasa, jagororin musulmi da na mabiya addinin yahudanci a kasar Faransa sun gudanar da wani zaman taro domin nuna rashin amincewa da cin zarafin musulmi da nuna msu kyama da ake a cikin kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na atlasinfo an bayyana cewa, jagororin musulmi da na mabiya addinin yahudanci a kasar Faransa sun gudanar da wani zaman taro domin nuna rashin amincewa da cin zarafin musulmi da nuna msu kyama da ake a cikin kasar ta faransa acikin lokutan nan.
Bayanin ya ci gaba da cewa wannan zaman taro zai tabo wasu daga cikin muhimman batutuwa da suka danganci rawar da musulmi suke takawa a dukkanin lamurra na zamantakewa a cikin faransa, da kuma wajabcin kawo karshen irin gaba da ake nuna musu a cikin kasar, musamman ganin cewa a halin yanzu addinin muslunci shi ne addini na biyu wajen yawan mabiya a Faransa.
Jagororin musulmi da na mabiya addinin yahudanci a kasar Faransa sun gudanar da wani zaman taro domin nuna rashin amincewa da cin zarafin musulmi da nuna msu kyama da ake a cikin kasar.
788390