Bangaren kasa da kasa, babban malamin mabiya addinin muslunci kuma mai bayar da fatawa akasar Belarus ya ziyarci babbar cibiyar bincike ta Noor da ke birnin Qom a jamhuriyar muslunci ta Iran, inda ya gane ma idanunsa muhimman ayyukan da ake gudanarwa awannan cibiya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, awani labari da ya samu daga shafin sadrawa na yanar gizo an habarta cewa, babban malamin mabiya addinin muslunci kuma mai bayar da fatawa akasar Belarus ya ziyarci babbar cibiyar bincike ta Noor da ke birnin Qom a jamhuriyar muslunci ta Iran, inda ya gane ma idanunsa muhimman ayyukan da ake gudanarwa a wannan cibiya da ke ayyukanta a bangaren yanar gizo.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo nacoe an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro mai taken hadin gwiwa tsakanin addnin muslunci da kuma yammacin turai, wanda za agudanar a babbar majalisar kungiyar tarayyar turai a birnin Bruccel na kasar Belgium, tare da halartar wakilai daga dukkanin bangarorin biyu.
Bayanin ya ci gaba da babbar manufar ita ce kara fito da mahangar addinin addinin kan muslunci kan lamurra na zamantakewa da siyasa, maimakon yadda ake kallonsa acikin mafi yawan kasashen turai, inda musulmi suke kokawa kan irin matsalolin da suke fuskanta a bangarori daban-daban, wanda hakan yana faruwa salkamakon rashin sanin hakikanin addini daga al’ummomin kasashen nahiyar turai.
788264