Bangaren kasa da kasa, an bude wata babbar cibiya ta tattaunawa tsakanin dukkanin mabiya addinai na kasar Lebanon, wadda ked a mazauni a yankin Rabiyya a arewacin birnin Beirut fadar mulkin kasar ta Lebanon, tare da halartar wakilai daga kungiyoyin addinai na Musulunci da kiristanci na kasar.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto daga bangaren yada labaransa na birnin Beirut a kasar Lebanon cewa, an bude wata babbar cibiya ta tattaunawa tsakanin dukkanin mabiya addinai na kasar Lebanon, wadda ked a mazauni a yankin Rabiyya a arewacin birnin Beirut fadar mulkin kasar ta Lebanon, tare da halartar wakilai daga kungiyoyin addinai na Musulunci da kiristanci na kasar ta Lebanon.
Wannan cibiya dai za ta mayar da hankali wajen gudanar da ayyukanta da suka danganci hada kan 'yan kasa da kuma sauran masu sha'awar shiga cikin harkokin yada fahimta juna tsakanin dukkanin mabiya addinai na kasar Lebanon, da nufin kara karfafa dangantaka tsakanin al'ummar kasar da aka sansu zama tare da juna a tsawon tarihi.
Bude wata babbar cibiya ta tattaunawa tsakanin dukkanin mabiya addinai na kasar Lebanon, wadda ked a mazauni a yankin Rabiyya a arewacin birnin Beirut fadar mulkin kasar ta Lebanon, tare da halartar wakilai daga kungiyoyin addinai na Musulunci da kiristanci na kasar zai taimaka matuka ga dukkanin bangarorin.
789832