Bangaren kasa da kasa, al'ummomin musulmi da na larabawa da yankin gabas ta tsakiya da kewaye sun mike tsaye domin kawo karshen mahukunta azzalumai masu yin hidima ga 'yan mulkin mallaka, saboda tunanin muslunci na asali.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an bayyana cewa, daya daga cikin manyan malaman addinin kuma masani kan harkokin shari'a Muhammad Nuri ya bayyana cewa, al'ummomin musulmi da na larabawa da yankin gabas ta tsakiya da kewaye sun mike tsaye domin kawo karshen mahukunta azzalumai masu yin hidima ga 'yan mulkin mallaka, saboda tunanin muslunci na asali, da kuma gudunmawar da juyin juya halin muslunci na Iran ya bayar wajen fadar da mutane.
Bayanin ya ci gaba da cewa, malamin ya bayyana cewa al'ummar musulmi da na larabawa da ke yankin sun sammu kyawawan darussa daga abin da suka gay a faru a Iran, inda mutane suka tashi suka ce tsarin addinin muslunci suke so, ba tsarin sarauta da 'yan mulkin malalaka suke mara wa baya ba, kuma daga karshen lamari al'umma ta yi nasara.
Al'ummomin musulmi da na larabawa da yankin gabas ta tsakiya da kewaye sun mike tsaye domin kawo karshen mahukunta azzalumai masu yin hidima ga 'yan mulkin mallaka, saboda tunanin muslunci da manzo ya zo da shi.
790871