Bangaren kasa da kasa, an rattaba hannu kan wata takardar yarjejeniya tsakanin jami'an Lexemburg da kuma cibiyar bunksa harkokin tattalin arzikin Musulunci, da nufin samun masaniya da kuma yin aiki da kwarewar da dukkanin bangarorin biu sukae da ita a fuskacin ayyukansu.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na paperjam cewa, an rattaba hannu kan wata takardar yarjejeniya tsakanin jami'an Lexemburg da kuma cibiyar bunksa harkokin tattalin arzikin Musulunci, da nufin samun masaniya da kuma yin aiki da kwarewar da dukkanin bangarorin biu sukae da ita a fuskacin ayyukansu na yau da kullum.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na al-islam an bayyana cewa, musulmin kasar Switzerland da suka musulunta za su gudanar da wani zama domin yin bitar irin ci gaban da suka samu bayan karbar addinin muslunci a matsayin addininsu, wanda kuma za su ci gaba da yin hakan a shekara-shekara domin samun karfafa gwiwar junansu.
Kasar Switzerland dai na daga cikin kasashen da suka bi sahun siyasar wasu kasashen turai ta nuna kyam aga addinin muslunci, inda suka gabatar da wani daftarin doka da ke neman a hana gina masallatai a kasar, kuma mambobin majalisa suka amince da hakan.
790888