IQNA

An Fara Taron Share Fage Na Ministocin Harkokin Waje Na Kasashen Musulmi A Jidda

15:36 - May 17, 2011
Lambar Labari: 2123922
Bangaren kasa da kasa; a ranar ashirin da biyar ga watan Urdebehesht ne na shekara ta dubu daya da dari uku da tis' in hijira shamsiya a birnin Jidda na kasar Saudiya ministocin harkokin waje na kasashen musulmi mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi suka fara wani taron share fage na taron shugabannin kungiyar .




Kamfanin dillancin labarai na Ikna ne da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ya watsa rahoton cewa; a ranar ashirin da biyar ga watan Urdebehesht ne na shekara ta dubu daya da dari uku da tis' in hijira shamsiya a birnin Jidda na kasar Saudiya ministocin harkokin waje na kasashen musulmi mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi suka fara wani taron share fage na taron shugabannin kungiyar . A taron share fagen ministocin harkokin kasashen musulmi da ke mambobi a kungiyar hadin kan kasashen musulmi za su tabo abubuwa masu yawa da suka hada irin ci gaba da kasashen suka samu a fuskoki daban-daban da suka hada tattalin arziki ,tsaro,siyasa,da zamantakewa da kuma ilimi da al'adu yayin da a dayan bangaren su tabo irin matsalolin da suke fuskanta musamman matsalar palsdinu da sauran kasashen musulmi.

792592

captcha