Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan yadda mata musulmi suke shiga cikin harkokin siyasa da zamantakewa a wasu kasashen nahiyar turai, musamman a kasashen Birtaniya da kuma da Faransa.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan yadda mata musulmi suke shiga cikin harkokin siyasa da zamantakewa a wasu kasashen nahiyar turai, musamman a kasashen Birtaniya da kuma da Faransa inda ked a mabiya addinin Musulunci da dama.
Bayanin ya ci gaba da cewa mata mabiya addinin muslunci a kasashen Faransa da kuma Birtaniya suna taka gagarumar a cikin harkoki da dama musamman na zamantakewa, a kan haka ne sukan gudanar da zama a kowace sheka a birnin Paris na kasar faransa domin yin bita kan irin ci gaban da suka samu ta wannan fuska a cikin shekara.
Za a gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan yadda mata musulmi suke shiga cikin harkokin siyasa da zamantakewa a wasu kasashen nahiyar turai, musamman a kasashen Birtaniya da kuma da Faransa.
793027