IQNA

Masu Ziyara A Birnin Karbala Sun Yi Kira Da A Gyara Makabartar Baki'a

13:00 - May 19, 2011
Lambar Labari: 2124958
Bangaren kasa da kasa, masu ziyara abirnin Karbala mai alfarma na kasar Iraki, sun kirayi mahukuntan wahabiyan kasar Saudiyya da su gyara makabartar Baki'a mai tsarki da ke birnin Madina mai alfarma, maimakon barin barin wurin a halin da yake ciki yanzu.



Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo an habarta cewa, masu ziyara abirnin Karbala mai alfarma na kasar Iraki, sun kirayi mahukuntan wahabiyan kasar Saudiyya da su gyara makabartar Baki'a mai tsarki da ke birnin Madina mai alfarma, maimakon barin barin wurin a halin da yake ciki yanzu, inda aka bar kabrukan a'imma da salihan sahabbai ba tare da gyara ba.

A wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na saphirnews an bayyana cewa, za a gudanar da wani zaman taro da zai yi dubi kan yadda mata musulmi suke shiga cikin harkokin siyasa da zamantakewa a wasu kasashen nahiyar turai, musamman a kasashen Birtaniya da kuma da Faransa inda ke da mabiya addinin Musulunci da dama.

Bayanin ya ci gaba da cewa mata mabiya addinin muslunci a kasashen Faransa da kuma Birtaniya suna taka gagarumar a cikin harkoki da dama musamman na zamantakewa, a kan haka ne sukan gudanar da zama a kowace sheka a birnin Paris na kasar faransa domin yin bita kan irin ci gaban da suka samu ta wannan fuska a cikin shekara.

794084
captcha