Bangaren kasa da kasa, a yau ne za akawo karshen gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasar hadaddiyar daular larabawa, wadda ke samun halartar makaranta daga sassa daban-daban na kasar, inda ake gudanar da gasar a bangaren karatun tartili.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakaltoo daga shafin sadarwa na yanr gizo na jaridar Albayan ta kasar UAE an habarta cewa, a yau ne za akawo karshen gasar karatun kur'ani mai tsarki ta kasar hadaddiyar daular larabawa, wadda ke samun halartar makaranta daga sassa daban-daban na kasar, inda ake gudanar da gasar a bangaren karatun tartili da kuma kaidojin karatu.
A wani labari da ya nakalto daga shafin yanar giz na atlainfo an bayyana cewa, babban daraktan cibiyar addnin muslunci da kuma babban masallacin birnin Lion na kasar Faransa Kamil Kabtan ya bayyana cewa, wannan masallacin da kowa da kowa ne, ba kamar yadda jami’an ma’aiktar tsaron kasar Amurka suka fada ba kan cewa wuri ne na taruwar ‘yan ta’adda da suke yin barazana ga nahiyar turai.
Bayanin ya ci gaba da cewa, dukkanin mabiya addinin muslunci suna hakki su zo su gudanar da lamurran ibada acikin masallaci daga ko’ina cikin duniya, kuma abin da jami’an na ma’aikatar tsaron kasar Amurka suka fada babu kamshin gaskiya a cikinsa, domin kuwa dukkanin mabiya addinin msulunci sun yi imani da zaman lafiya tsakaninsu da sauran mabiya addinai.
795060