Kamfanin dillancin labarai na Ikna da ke kula da harkokin kur'ani a nan jamhuriyar musulunci ta Iran ne ya watsa wahoton cewa; : taron kan addinin musulunci a kasar Italiya inda za a yi nazari kan mahanga da jikonsa a ranar biyar ga watan Khurdad shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya a babban masallacin da ke birnin Rom fadar mulkin kasar ta Italiya. Hukumar da ke kula da harkokin ilimi da al'adun musulunci Asesko a kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta shirya gudanar da wannan taro inda mahukumata da jami'an gwamnatio da jami'an da ke kula da al'adu da wakilan hukumomin musulunci a biranai daban-daban na kasar Italiya da kasashe masu makobtaka da Italiya za su halarci wannan taro.
795487