IQNA

Zanga-Zangar Mutanen Bahrain Ta Lumana Da Neman Sauye-Sauyen Siyasa Ce

16:45 - May 22, 2011
Lambar Labari: 2126576
Bangaren kasa da kasa, babban malamin addinin musulunci na kasar Bahrain Ayatollah Isa Kasim ya bayyana cewa, zanga-zangar da mutanen kasar Bahrain suke gudanarwa ta neman sauyi ce a fagen siyasar kasar, kuma har yanzu ana gudanar da ita ne ta hanayar lumana.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wani labari da ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin al-alam an bayyana cewa, babban malamin addinin musulunci na kasar Bahrain Ayatollah Isa Kasim ya bayyana cewa, zanga-zangar da mutanen kasar Bahrain suke gudanarwa ta neman sauyi ce a fagen siyasar kasar, kuma har yanzu ana gudanar da ita ne ta hanayar lumana, duk kuwa da yadda mahukuntan kasar suke hankoron canja fuskar zanga-zangar.
Malamin ya ci gaba da cewa babban abin takaici ne yadda al’ummomin duniya suka yi gum da bakunansu kan ta’asar da mahukuntan Bahrain suke tafkawa kan fararen hula masu neman sauyi a kasar, wani abu mafi muni ma shi ne yadda wasu bangarori suke baiwa abin fuska ta mazhabanci da bangaranci, domin kawai a haramta ma al’umma hakkokinta.
Babban malamin addinin musulunci na kasar Bahrain Ayatollah Isa Kasim ya bayyana cewa, zanga-zangar da mutanen kasar Bahrain suke gudanarwa ta neman sauyi ce a fagen siyasar kasar, kuma har yanzu ana gudanar da ita ne ta hanayar lumana da ruwan sanyi.
795391

captcha