IQNA

Wani Zaman Taro Kan Aikewa Da Jirgin Ruwa Da Ke Dauke Da Taimako Zuwa Gaza

16:47 - May 22, 2011
Lambar Labari: 2126578
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da wani zaman tattaunawa dangane da aikewa da wani jirgin ruwa da ke dauke da taimako zuwa ga al’ummar Gaza, domin karya takunkumin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kakaba wa al’ummar yankin domin zalunci da danniya.
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto wani rahoto da ke cewa, za a gudanar da wani zaman tattaunawa dangane da aikewa da wani jirgin ruwa da ke dauke da taimako zuwa ga al’ummar Gaza, domin karya takunkumin da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kakaba wa al’ummar yankin domin zalunci da danniya, taron dai zai gudana ne abirnin paris fadar mulkin kasar Faransa.
A wani labari da ya nakalto daga shafin sadrawa na yanar gizo na algeriesoir an bayyana cewa, an gudanar da sallar juma’a abirnin Rom fadar mulkin kasar Italia a babban dandalin da ke tsakiyar birnin, domin nuna rashin amincewa da matakin da mahukuntan suka dauka na kin bayar da izinin gina masallaci a birnin wanda ake kallaonsa amatsayin babban birnin na mabiya addinin kirista.
Bayanin ya ci gaba da cewa mabiya addnin muslunci na kasar Italia musamman ma mazauna birnin Rom, suna ganin cewa bisa la’akari da yawan da suke da shi a kasar, daidai da ddokokin da aka amince da su auna da ahakkin su mallaki babban masallacin juma’a a cikin birnin Roma, kuma sun aike da takardun neman izini kan hakan, amma har yanzu mahukunta ba su ce komai ba ko daukar wani mataki.
795601

captcha